Gwamnatin Kano za ta karfafa hulda da kafafen yada labaran internet

Daga Hauwa Sani, Kano

Gwamnatin Kano ta Jaddada aniyar tana karfafa hadin gwiwa da kafafen yada labarai na internet Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, kwamared Ibrahim Abdullahi waiya ne ya bayyana hakan a yayin taron masu Ruwa da tsaki da kungiyoyin kafafen yada labarai na intanet a Kano, inda yace manufar hakan Shi ne domin inganta yada sahihan labarai ga Al'umma.
Waiya ya Jaddada muhimmancin kafafen yada labarai na internet wajen isar da labarai cikin gaggawa ga Al'ummar duniya, a Dan haka ya tabbatar musu da cewa gwamnatin injiniya Abba kabir yusif, a shirye take wajen yin aiki tare dasu domin isar da manufofi da shirye shiryenta ga Jama'a.
A cewar Kwamishinan, "Ku manyan a bokan Huldar gwamnati ne a fannin yada labarai la'akari da rawar da kuke takawa batada misali, saboda haka gwamnatin mu zata tabbatar da cewa kuna cikin shirye shiryen ta, ciki harda tsarin bada horo da sauran matakan bunkasa kwarewa don inganta aikin jarida.
Toh sai dai kuma ya bukaci Yan jaridar su kiyaye ka'idojin aikin jarida ta hanyar mutunta hakkin kowanne Dan kasa tare da yada sahihan labarai, mafari kenan da ya nemi hadin Kan kungiyoyin domin karfafa tasirinsu a fannin yada labarai ga Jama'a.
Sanarwar da daraktan aiyukan yau da kullum a ma'aikatar yada labarai ta jihar Kano, Sani Abba yola ya aiko wa jaridar GTR Hausa tace a jawabansu daban daban wakilan kungiyoyin sun jinjinawa Kwamishinan bisa Yadda ya fahimci muhimmancin kafafen yada labarai na intanet.
A karshe sun bukaci goyan bayan gwamnati musamman a fannin Kula yarjejeniyar yin aiki tare don tabbatar da cigaban ayyukansu , tare da Samar da horo ga sabbin Yan jarida da wadanda ke aiki a halin yanzu.