Yanda bikin ranar mata ta duniya ta kasance, da tarihin wannan rana.

BY JAMILA ADAMU BAUCHI.

Bikin Ranar mata ta duniya ta samo asaline tun  fiye da karni Guda , taron farko da aka gudanar  anyi shine a ranar 28 ga Fabrairu, 1909, a birnin  New York,  na kasar Amurka, wanda Jam'iyyar Socialist Party of America  ta shirya.  Duk da haka, ra'ayin ranar mata ta duniya ya sami ci gaba a cikin 1910 lokacin da Clara Zetkin, 'yar gurguzu ta Jamus, ta ba da shawarar a taron kasa da kasa na mata masu ra'ayin gurguzu a kasar Denmark.

An yi bikin ranar mata ta duniya ta farko a ranar 19 ga Maris, 1911, a a kasashen Austria, Denmark, Jamus, da kuma Switzerland, tare da mutane sama da miliyan ɗaya suka halarta,  Mata sun bukaci ‘yancin kada kuri’a, da yaki da wariyar jinsi a wuraren aiki, da kuma rike mukaman gwamnati.

Bayan wassu shekaru bikin ranar matan ta duniya ta samu karbuwa a wasu kasashe da suka hada da “Rasha”  “Sin”  da “Amurka”.  A cikin shekara ta 1917, matan Rasha sun taka muhimmiyar rawa a juyin juya halin Rasha, kuma  hakan ta sanya ranar mata ta duniya ta zama ranar hutu ta kasa a Rasha.

 A cikin shekara ta 1960, ranar mata ta duniya ta zama muhimmiyar rana ta gwagwarmayar mata, Majalisar Dinkin Duniya ta fara bikin ranar mata ta duniya a 1975, kuma a cikin 1977, Majalisar Dinkin Duniya ta gayyaci kasashe, mambobin Majalisar Dinkin Duniya don ayyana ranar 8 ga Maris a matsayin ranar 'yancin mata da zaman lafiya ta duniya.

 A ana bikin ranar mata ta duniya a kasashe da dama ta duniya, inda kungiyoyin kare hakkin mata, gwamnatoci, da daidaikun jama'a suka taru domin inganta Mata tare da  karfafawa mata gwuiwa, daidaito da kuma 'yancin dan adam.

Taken bikin na bana shine,  "hanzari wajen daukan matakan gyara” don daidaiton jinsi. Wannan taken  ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai wajen cimma daidaito tsakanin jinsi, da magance tafiyar hawainiya, da karfafawa mata da 'yan mata a duniya baki daya.  Rana ce da ake sanin mata bisa nasarorin da suka samu ba tare da la’akari da rarrabuwar kawuna ba, ko na kasa, kabila, harshe, al’adu, tattalin arziki ko siyasa ba.

Kana ranar ta wannan shekra ya kara laakari  wajen samar da  “Hakkoki”  Ga Duk Mata da 'Yan Mata:  Daidaito.  Karfafawa.”  Taken wannan shekara yana kira da a yi aiki don buɗe daidaitattun haƙƙoƙi, iko da dama , Ban da wannan kuma, bikin na wannan shekarar ta 2025 wani muhimmin lokaci ne yayin da ake bikin cika shekaru 30 na wani shelar da aka cimma kan hakkokin mata  a birnin Beijing. 

Ranar wata dama ce ta amincewa da ci gaban da aka samu wajen daidaiton jinsi, tare da bayyana ayyukan da har yanzu ya kamata a yi. 

 Duk da manyan nasarorin da aka samu, mata da 'yan mata suna ci gaba da fuskantar ƙalubale masu yawa, gami da tashin hankali, wariya, da rashin daidaiton tattalin arziki da dai sauransu.

 Kasashe da dama ciki hard a Nigeria sun kaddamar da tsare-tsare da dama don hanzarta aiwatar da daidaiton jinsi, wanda ya hada da Global Digital Compact, wanda ke da nufin kawo karshen rarrabuwar kawuna na jinsi, da kuma kawar da cin zarafi na jinsi.

Wannan yana gwada cewa akwai bukatan Karfafa muryoyin mata don ƙalubalantar  ƙa'idodi da ayyuka na wariya, da haɓaka daidaiton jinsi a cikin al'ummar ku,

Kana da batun bada dama ga mata na samun damar rike madakun iko na shugabanci.

Gwamnatoci da ƙungiyoyi da yawa a faɗin duniya suna karrama wannan biki saboda gudunmawar 'ya'ya mata da kuma tabbatar da 'yancinsu.

Tun tale-tale dai, mata da 'yan mata ba su cika samun dama iri ɗaya da ta maza ba, kuma har yanzu mata na fuskantar wariya, kodayake al'ummomin na faɗi-tashin ganin an canza hakan.

Haj jummmai adamu wata yar gwagwarmaya ce na hakkin mata a Nigeria kuma ta bayyana irin yadda matan ke samun dama kan harkokin mulki da shuganci tare da cewa ya yi karanci. 

Wannan yana gwada cewa du da irin matakan da ake daukan naganin an daidaita al'amura, akwai sauran rina a kaba , adon haka akwai bukatar dake akwai ga kungiyoi kare hakkin mata, gwamnatoci, da dai daikun al`umma da sake lale da kuma jadda da taken bikin na bana wato hanzarta daukan matakan gyara, wajen kare hakkin mata , dai daita jinsi, rike shugabanci da kuma cin zarafi.

Ku biyo mu a shafin mu na Facebook and Skylink Multimedia Ltd. Don Jin shirin mu na Radio akan wannan Rana. 

Ko ku latsa kasa don Jin shirin ta Skylink Radio 👇.